3 Satumba 2020 - 10:51
​Za A Kashe Dala Biliyan 3.1 Wajen Bunkasa Hukumar Kwastam A Najeriya

Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta ba da lamunin fitar da Dala biliyan 3.1 domin karasa aikin inganta harkokin gudanarwa a Hukumar Hana Fasakwauri ta Najeriya.

ABNA24 : Rahotanni daga Najeriya sun habarta cewa, Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Ahmed, ita ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan halartar zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa da Abuja.

Hajiya Zainab ta ce makasudin hakan shi ne mayar da dukkan harkokin gudanarwa na Hukumar Kwastam su koma amfani da fasahar zamani musamman bangaren sadarwa da tattara bayanai.

Haka nan kuma ta bayyana cewa yarjejeniyar kwangilar aikin na tsawon shekara 20 kudadenta za su fito ne daga masu zuba jari da kudaden shiga da ake sa ran samu daga Hukumar, wadanda sun tasar ma Dala biliyan 176.

Hukumar kwastam a Najeriya bangare ne da ke da matukar muhimmanci ga gwamnatin kasar ta fuskoki da dama, baya ga hana fasakwaurin kayayyaki, tana kuma samar da makudan kudaden shiga ga gwamnati.

342/